A wani hukunci da kotun mai alkalai biyar ta yi kotun ta bayyana zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar Ribas a matsayin mara inganci saboda saba dokar zabe.
Mai shari’a Jamilu Tukur wanda ya karanto hukuncin ya bayyana cewa hukumar zabe ta jihar Ribas abinda ta yi rashin bin doka da ka’idojin zabe ne, saboda hukumar zaben ta ci gaba da yin rajistar masu kada kuri’a bayan ta bayyana ranar gudanar da zabe.
A wani labarin ma, Kotun kolin ta kuma umurci bangaren majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Martins Amaewhule da sauran zababbun ‘yan majalisar da su ci gaba da zama a majalisar.
Bangaren da Amaewhule ke jagoranta dai na biyayya ne ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Kazalika kotun kolin ta tuhumi kotun daukaka kara ta Abuja da yin watsi da umurnin farko na dakatar da sakin kudaden ga Jihar Rivers, sakamakon gazawar gwamnan jihar Siminalaye Fubara na kin sake gabatar da kudirin kasafin kudin jihar na shekarar 2024 a gaban majalisar dokokin jihar karkashin jagorancin Martins Amaewhule.