Kotu ta dage sauraren shari'ar Ganduje da matarsa da ake zargi da almundahana


Wata babbar kotu a jihar Kano ta dage sauraren karar da aka shigar kan shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutane bakwai, bisa zargin cin hanci da almundahanar kudade har zuwa ranar 15 ga watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, zarge zarge takwas ne gwamnatin jihar Kano ta gabatar kan Ganduje, da matarsa Hafsat Umar.

Sauran wadanda ake kara sun hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, da kamfunnan Lamash properties Limited, da Safari Textiles Limited da kuma Lasage General Enterprises Limited.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp