Mai bai wa shugaban Nijeriya Bola Tinubu shawara kan yada labarai Daniel Bwala, yayi zazzafan martanin ga Nasir El’rufa’i inda yace ko kujerar Sanata Nasiru Elrufa'i ba zai iya ci a Kaduna ba, domin siyasarsa ta labewa cikin rigar wani jagora ce.
Bwala ya yi martanin ne a wata fira da gidan talabijin na TVC, inda ya ce tasirin siyasar El-Rufai yana da nasaba da hadakarsa da wasu jagorori, nasarar da El'rufa'i ya samu a siyasa har ya zama gwamnan Kaduna, ya laɓe ne da guguwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma saboda Buhari ne aka sake zabensa karo na biyu, a don haka a yanzu ba zai iya cin zaben ko da Sanata ba.
A 'yan kwanakinnan dai tsohon gwamnan jihar Kaduna na yawan sukar gwmnatin shugaba Tinubu da kuma jam'iyyar APC, duk da kasancewarsa dan jami'yyar.
Category
Labarai