Kayan aikin dake filin jirgin saman Legas tsofaffi ne, akwai buƙatar yin gyara cikin gaggawa - Ganduje

 

Ganduje

Shugaban hukumar gudanarwa ta hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya FAAN, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jaddada bukatar gyara filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammed cikin gaggawa saboda kayan aikin da ke filin jirgin saman sun tsufa.

Yayin ziyara ta farko da ya kai tare da rakiyar babbar daraktar hukumar ta FAAN, Olubunmi Kuku, Ganduje ya tabbatar da cewa yawancin kayan aikin filin jirgin sun lalace.

Ganduje ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar za ta hada kai da hukumomi domin inganta filayen jirgin sama ta yadda za su yi gogayya da na duniya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp