![]() |
Tambarin hukumar NABTEB |
Hukumar shirya jarabawar NABTEB ta fitar da sakamakon jarabawar da aka yi a watannin Nuwamba zuwa Disambar shekarar 2024, inda sama da kaso 67 cikin 100 na waɗanda suka rubuta suka lashe darusa biyar-biyar zuwa sama.
Mukaddashin magatakardan hukuma Dr. Nnasia Asanga, ne ya sanar da hakan ranar a Benin.
Yace mutane dubu 44 da 226 ne suka rubuta jarabawar, yayin da dubu 29 da 880 daga cikinsu suka samu duk abinda ake bukata.