Kamfanin mai NNPCL ya musanta zargin sayar da fetur mai saurin konewa


A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye, NNPCL ya mayar da martani a kan wani bidiyo da ke yawo cewa man fetur na gidan man kamfanin bai dadewa.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta na wani mai amfani da shafukan sadarwa ya yi ikirarin cewa ya sanya litar mai a cikin janareta biyu, daya na matatar Dangote daya na NNPC.

Sai dai man NNPC ya kare cikin minti 17, yayin da na Dangote ya kare cikin minti 33.

A martanin da ya mayar, kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya ce man da yake sayar wa na matatar Dangote ne.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp