Gwamnatin jihar Zamfara ta ce ta bankado ma'aikatan bogi 2,363 bayan aikin tantance ma'aikatan jihar da aka gudanar, tare da like hanyar zurarewar kudin gwamnati da suka kai naira miliyan 193.6 a kowane wata.
Gwamna Dauda Lawal ne ya kafa kwamitin karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Zamfara a watan Augustan 2024 da manufar tantance ma'aikatan jihar.
Wani bayani da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Idris, ya ce a yayin aikin an gano kananan yara 220 da aka sanya cikin ma'aikatan jihar kuma suke karbar albashi.
Category
Labarai