![]() |
Janar Abdulrahman Tiani |
Ministar kwadago ce ta Nijar madam Aissata Abdoulaye Tondi a cikin wata doka da ta dauka ta bayyana kawo gyaran fuska ga lokutan aikin
Da zaran watan azumin Ramadan din ya kama dokar ta ce ma'aikatan za su hau aiki ne daga karfe 8 na safe zuwa karfe 4 da rabi na marece daga ranar litinin zuwa alhamis maimakon tashi karfe 5 da rabi kafin azumi
Ranar Juma'a kuwa za a sauka daga aikin ne a karfe daya na rana