Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu mutane ukku


Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da sanata da wasu yan majalissu na jam'iyyar mutum 4 wadanda suka hada da Sanata Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu, Alhaji Abdullahi Sani Rogo, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Rogo, Alhassan Rurum mai wakiltar Rano da Kibiya, da kuma Ali Madakin Gini mai wakiltar mazabar Dala a majalisar wakilai ta Nijeriya.

Wannan sanarwa ta fito ne daga shugaban jam’iyyar na jiha Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano.

A cewar shugabanjam’iyyar, an zabi ‘yan majalisar dokokin ne a karkashin jam’iyyar NNPP amma a baya-bayan nan an hango su sun tsunduma cikin ayyukan da suka saba wa muradun jam’iyyar tare da karya ka’idojin jam’iyyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp