Idan har za a yi zabe na gaskiya, to babu shakka nine zan lashe zaben 2027 - Sanata Rabi'u Kwankwaso

 

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP tsagin mai littafi, ya ce jam'iyyarsa za ta kayar da jam'iyya mai mulkin Nijeriya APC da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP da sauran jam’iyyu a kasar idan aka yi zaben.

Kwankwaso wanda ke jawabi a wurin taron shugabannin jam'iyyar da ya gudana a Abuja, ya yi nuni da cewa ‘yan Najeriya ba su ji dadin salon mulkin da ake yi a yanzu ba.

Yace 'yan Nijeriya na sane da matsalolin da PDP ke fuskanta, da kuma halin da salon mulkin jam'iyyar APC ya jefa su, a saboda haka ya yabawa goyon bayan da 'yan kasa suka bashi a zaben 2023, inda ya ba su tabbacin cewa a 2027 shine zai zama shugaban Najeriya.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp