Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya INEC ta bukaci majalisa ta yi dokar haramta zuwa da kudade masu yawa a rumfunan zabe domin magance matsalar sayen kuri'a da kuma magudin zabe.
Daraktan sashen dokoki na hukumar Tanimu Muhammed, SAN, ne ya yi wannan kiran a yayin wani taron kan sake gyaran dokokin zabe da kwamitin majalisar wakilai kan zabe ya shirya a Abuja.
Tanimu Muhammed ya bukaci 'yan majalisa da su fito da dokar da zata saka naira dubu hamsin a matsayin mafi karancin kudin da mutum zai iya rika wa a kusa da rumfunan zabe.
Category
Labarai