Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da wani film mai suna 'Zarmalulu' tare da gayyatar dukkannin wadanda suka fito a cikinsa domin jin ba'asi, biyo bayan zargin yin amfani da kalmar badala a matsayin sunan film din.
Hukumar karkashin jagorancin Alhaji Abba El-Mustapha ta ce ta karbi korafi daga wasu yan kishin jihar Kano akan wannan film din bisa zargin rashin ma'ana.
Abba El-Mustapha ya bayyana damuwarsa akan lamurin tare da bayar da umarnin dakatar da film din, haka kuma ya gayyaci dukkannin wadanda ke da ruwa da tsaki a shirin.
A cikin wata sanarwa daga jami'in hulda da jama'a na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman da ya aike wa DCL Hausa, ta ce hukumar na da hurumin dakatar da dukkanin wani fim da ba ta gamsu da yadda aka shirya shi ba, tare da ladabtar da duk wanda ta samu da yin abin da bai kamata ba a cikin kowane fim.
Category
Labarai