Hukumar NDLEA ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Kogi

NDLEA 

Hukumar hana da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA reshen jihar Kogi ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Lokoja babban birnin jihar a ranar Laraba.

Wakilin shugaban hukumar NDLEA Brig. Janar Mohammed Buba Marwa a wajen taron, daraktan ayyuka da bincike na hukumar ta NDLEA, Ahmed Suleiman Ningi, ya jaddada illar da ke tattare da irin wadannan haramtattun magunguna.

Ya ce idan aka bari mutane na amfani da haramtattun magunguna irin haka,yana iya kara tsananta kalubalen tsaro a cikin kasar.

Kwayoyin da aka lalata sun hada da, Tramadol, Rohypnol, Diazepam, Exol-5, Pentazocine da  Cocaine.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Umah Mustapha Yahuza, ya bayyana cewa an kama motoci 24 na masu safarar miyagun kwayoyi tare da kwacesu. 

Ya bukaci hadin kan al'umma wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi, ya kuma bayyana cewa akwai karin tan biyar na haramtattun kwayoyi har yanzu ana ci gaba da shari’a akai.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp