Hukumar NAFDAC ta rufe shaguna 3,000, tare da kama manyan motoci 14 da jabun magunguna

 

NAFDAC

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya NAFDAC ta rufe shaguna 3,000 a Legas tare da kwace tireloli 14 na jabun magunguna da wa’adinsu ya kare a Onitsha da wasu sauran wurare.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta ce ta manyan motocin dakon kaya guda 14 da ke dauke da jabun magungunan ta a Legas.

Babbar daraktar hukumar ta NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta kuma bayyana cewa jami’an tsaro sun bankado wasu manyan shaguna da ke mãƙare da jabun magunguna a Aba a karshen mako.

A cewar sanarwar, yayin da jami'an ta suka kai sumame a wani katafaren rumbun ajiyar magunguna da ke kauyen Umumeje, Osisioma Ngwa a Onitsha, inda ake dawo da magungunan da amfaninsu ya kare tare da sabunta su domin sake sayar da su, sunyi nasarar kamawa tare da rufe rubunan ajiyar irin wadannan magunguna.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp