Hukumar NAFDAC mai kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya ta bukaci a fara hukuncin kisa ga dilolin kwaya

 


Babbar daraktar hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye a wata zantawa da gidan talabijin na Channel a ranar juma’ar nan, tace wannan matakin kadai ne zai kawo karshen safarara miyagun kwayoyi duba da yadda suke silar mutuwar yara.

Mojisola  ta nanata cewa hukunci kisa ya zama dole ga wadannan bata gari.

Ta kuma nemi goyon bayan majalisa da kuma bangaren shar'ia domin yin wannan dokar.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp