Hukumar Kwastam ta Najeriya, ta kama wata kwantena mai kafa 40 dauke da busasshen fatar jaki guda 4,410 wanda kudinsa ya kai kusan Naira biliyan 4.236.
Kwanturola Kola Oladeji ya bayyana haka a Lagos inda ya kara da cewa an kama wasu mutane shida da ake zargi da safarar haramtattun kayayyaki.
Haka kuma an kwace wasu manyan motoci guda 21 da kudinsu ya kai Naira miliyan 561.3 daga hannun wasu da ake zargin masu fasa kwaurin ne da ke gudanar da ayyukansu a yankin Kudu maso Yamma.