Hukumar kididdiga a Nijeriya NBS ta bayyana cewa farashin kayayyaki a kasar ya sauka zuwa kashi 24.48 a cikin watan Janairun shekarar 2025
Shugaban hukumar ta NBS, Prince Adeyemi Adeniran ne ya bayyana hakan a yayin ganawar sa da manema labarai a ranar Talata a Abuja.
Shugaban ya ce sabuwar kididdigar ta biyo bayan saukar da farashin kayayyaki a Nijeriya ,musamman a watan Janairun shekarar 2025.