Hukumar JAMB ta ce ba za ta kara wa'adin yin rajistar jarabawar ba idan aka wuce 8 ga watan Maris

 


Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare ta JAMB, ta ce ba za ta tsawaita lokacin yin rajistar jarrabawar ta shekarar 2025 ba bayan ranar 8 ga Maris.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dr Fabian Benjamin ya raba wa manema labarai a Abuja.

Benjamin ya ce wa'adin rajistar da ya fara ne daga ranar 3 ga Fabrairu, kuma zai kare ne a ranar 8 ga Maris, 2025.

Sanarwar ta yi kira ga duk wadanda ke son zana jarrabawar da su yi rajista cikin gaggawa dan hukumar ba za ta kara wa'adi ba.

Sanarwar ta kara da cewa zuwa yanzu, sama da mutum miliyan 1.5 ne suka yi nasarar yin rajistar, wadanda suka yi daidai da hasashen hukumar a shekarar 2025.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp