![]() |
Hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya NAHCON, ta bukaci masu zuwa aikin hajji da har yanzu ba su kammala biyan kudi ba, da sauran musulman Nijeriya da ke shirin zuwa aikin hajjin 2025 da su kammala biyan kudin su,inda ta ce ta yi nasarar samar da gurbi sama da dubu 52,000 na aikin hajji, don haka, ana ci gaba da yin rajista har a cike guraben da aka ba ta.
A cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktar yada labarai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar, ta bukaci dukkan mutanen da ke da sha’awar zuwa aikin Hajji da su kammala biyan kudinsu, ta ce da zarar an cike gurbin da aka bai wa hukumar ba za ta sake karbar kudin kowa ba.
Sanarwar ta ce gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Zulum, ya tabbatar wa shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman da sauran jami’an hukumar, kan kudirinsa na tallafa wa nasarar aikin Hajjin 2025.
Ya yi wannan alkawarin ne a yayin ziyarar da ya kai hedikwatar hukumar inda ya karfafa gwiwar mambobin kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas da su hada kai da NAHCON wajen ganin an gudanar da aikin Hajji cikin nasara da nasara.
Zulum ya yi alkawarin hada kan takwarorinsa gwamnonin a kungiyar gwamnonin Nijeriya domin su taimaka wa alhazansu wajen daidaita farashin Hajji a kan kari.