![]() |
Hon. Nasir ja'oji |
A wani yunkuri na bunkasa ilimi a karamar hukumar Taruni,Hwanarabil Nasir Aminu Bala Ja’oji ya bayar da tallafin karatu zuwa kasashen waje ga ‘yan asalin karamar hukumar Tarauni guda 20 da suka cancanta a jihar Kano.
Shirin wanda kungiyar Ja’oji Organisation ke jagoranta, zai baiwa wadanda suka ci gajiyar tallafin damar samun digiri na biyu a kasashen ketare, tare da basu ilimi da kwarewa da gogewa.
Da yake jawabi a wajen Hon. Ja’oji, wanda memba ne a majalisar gudanarwa ta Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Potiskum, ya jaddada muhimmancin ilimi wajen ci gaban kasa, inda ya bayyana cewa tallafawa matasa zai taimaka wajen gina rayuwar su tare da samun kwararrun ma’aikata a Nijeriya.
Ya bayyana cewa shirin bayar da tallafin karatun na da nufin samarda damammaki ga matasan Nijeriya,don suyi fice a duniya, da inganta rayuwarsu.