Hisbah ta haramta ayyukan gidajen rawa a Katsina

 


Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta haramta duk wani aikin gidajen casun Nightclub dare a fadin jihar, ta ce tsarin ya yi daidai da addinin Musulunci.

Babban Kwamandan Hisbah na jihar Dakta Aminu Usman Abu-Ammar ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ya bayyana cewa dole ne masu gidajen rawa su rufe gidajensu domin dakile munanan dabi’u, da kare mutuncin al’umma, da magance matsalolin tsaro a jihar.

Hukumar ta yi gargadin cewa duk wanda ya karya doka za su fuskanci hukunci mai tsauri.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp