Har yanzu Nijeriya laluben shugabanni nagari take yi - Sheikh Gumi

Sheikh Gumi

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Mahmoud Gumi, ya ce har yanzu Nijeriya na neman shugabannin da za su ciyar da kasar gaba.

A cewarsa, irin wadannan shugabanni su ne wadanda ke fifita jin dadin ‘yan kasa fiye da tara dukiya.

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin bikin karramawa da kungiyar tsofaffin daliban makarantar Sultan Bello (SUBOPA) ta shirya domin karrama mambobinsu guda biyu Manjo Janar Abdulmalik Jibrin (Rtd) da Birgediya Janar Abdulkadir Gumi (Rtd) wanda ya samu mukamin gwamnati kwanan nan. 

Gumi ya bayyana Manjo Janar Jibrin a matsayin hafsan soja mai himma, da’a, da kuma kwazo a lokacin aikin sa, inda ya ce Nijeriya na bukatar mutane irinsa a matsayin shugabanci saboda jajircewa da kishin kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp