![]() |
Carlo Ancelotti |
Ancelotti ya bayyana hakane a yayin wani taron manema labarai a ranar Litinin.
Wannan shi ne karo na hudu a jere da kungiyoyin biyu za su fafata a matakin bugun falan daya a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wanda zai bai wa wanda ya samu nasara zuwa zagaye na goma 16.
A karawar karshe da kungiyoyin suka yi, Madrid ta doke Man City a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan fafatawa da aka yi a cikin wasan.
Sai dai Real Madrid a wannan lokaci na fama da matsalar 'yan wasa, wadanda mafi yawanci ke jinya sakamakon rauni da suke fama da shi, abinda wasu ke ganin ya bai wa kungiyar matsala a karawar.