![]() |
Shugaba Tinubu |
Mai baiwa shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ta bayyana haka a taron shugabannin kasashen Afirka kan makamashi da aka yi a Dar es Salaam na kasar Tanzania, inda Nijeriya ta gabatar da wani shiri na dala biliyan 32 da nufin bunkasa wutar lantarki nan da shekarar 2030.
A cewarta Nijeriya na kokarin warware yin wasu sauye sauye masu inganci don jawo hankalin masu zuba jari zuwa kasar musamman ta fuskar makamashi.
Ta ce daya daga cikin manyan kalubalen da ake neman warwarewa a cikin 'yan watanni masu zuwa shine canza farashin wutar lantarki don ci gaba da samun kudaden shiga.