Ministan Noma da albarkatun kasa Abubakar Kyari ne ya bayyana bukatar hakan a ranar Talata, a yayin wani bikin noman alkama da aka gudanar a kauyen Dabi dake karamar hukumar Ringim ta jihar Jigawa.
Ministan ya bayyana takaicinsa kan yadda wasu 'yan kasuwa suka ki sauke farashi duk da saukowar kayayyaki, yana mai bayyana hakan a matsayin rashin kishin ƙasa.
Ya ce gwamnatin tarayya tana sane da saukar farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwanni, musamman na kayan masarufi kamar su gari, sukari, shinkafa da taliya.
Amma duk da haka wasu, masu yin burodi, da masu shaguna a cikin Unguwanni sun ki sauke farashin kayyayyakin amfanin yau da kullum, a saboda haka ya yi kira da su sauke farashi kamar yadda yake sauka a wasu kasuwanni.