Sojojin da ke mulki a Jamhuriyar Nijar sun ce za su shirya wani babban taron kasa domin saka ranar da gwamnatin sojin za ta mika mulki.
Ministan cikin gida na Nijar ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka yada a gidan talabijin na kasar, inda ya ce taron zai some ne daga rana 15 zuwa 19 ga watan Fabrairu, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tun bayan juyin mulkin 2023 da sojojin suka yi wa gwamnatin Mohamed Bazoum, shugaban gwamnatin sojin kasar Janar Abdourahamane Tiani ya sanar da cewa shekaru uku sojojin zasu yi su mika mulki, sai dai gwamnatin bata koma maganar ba sai a wannan lokaci.