Gwamnatin Nijeriya za ta kafa wata rundunar da za ta hana lalata na'urorin lantarki


Gwamnatin Nijeriya ta ce za ta kafa runduna ta musamman da za ta kare na'urorin samar da lantarki dake fadin kasar.

Ministan cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hakan a cikin shirin barka da safiya na gidan talabijin na Channels wanda aka yi a wannan jumu'ar.

Ya ce rundunar wadda za a samar daga cikin jami'an hukumar bayar da tsaro ga farin kaya ta Civil Defence, za su hana lalata kayan lantarki na kasar da ake yi, lamarin da ke haifar da lalacewar wutar lantarki a fadin kasar.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp