Gwamnatin Nijeriya ta musanta zargin babban jami'in kamfanin Binance Tigran Gambaryan wanda ya shafe watanni takwas yana tsare a hannun hukumomin Nijeriya bisa zargin rashawa.
Gambaryan wanda dan kasar Amurka ne, an sake shi bayan da gwamnatin kasar ta shiga tsakani, sai dai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya zargi gwamnatin Nijeriya da tsare shi ba bisa ka'ida ba.
Ya kuma yi zargin cewa wasu 'yan majalisa uku sun nemi ya basu cin hanci na dala miliyan 150.
A martanin gwamnatin, ta hannun ministan yada labarai Mohammed Idris, ta ayyana kalaman a matsayin yunkurin yada labaran karya.
Category
Labarai