Ministan ayyuka David Umahi, ya ce nan da wani lokaci za a kafa shingen karbar haraji a kan titunan gwamnatin Nijeriya, domin tabbatar da an kula da titunan yadda ya kamata.
David Umahi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake duba aikin hanyar Abuja-Kaduna.
Ya kara da cewa gwamnati na son amfani da hukumomi masu zaman kansu domin inganta titunan Nijeriya ta yadda al'umma za su ci gaba da amfana da su
Category
Labarai