Gwamnatin Nijeriya na shirin daidaita farashin wutar lantarki ga masu matakin band B da band C

 

Adebayo Adelabu

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ta daidaita farashin wutar lantarki a wani mataki na magance tsarin biyan kudi tare da karfafa gwiwar mas saka hannun jari a bangaren wutar lantarki.

Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ne ya bayyana haka a ci gaba da gabatar da shirin hadin gwiwa na tsarin samar da wutar lantarki a Nijeriya ranar Alhamis a Abuja.

Ministan ya ce karkashin tsarin da ake yi yanzu, kwastomomin da ke band B, wadanda ke samun wutar lantarki ta awanni 18 zuwa 17, suna biyan Naira 63 a kowace kilowatt, yayin da wadanda ke Band A, ke da karin sa’o’i biyu kacal, ake karbar Naira 209.

Adelabu ya bayyana hakan a matsayin rashin adalci kuma ya jaddada bukatar daidaita tasarin kuɗin don samar da ingantaccen tsarin farashin wutar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp