![]() |
Muhammadu Buhari |
Wani jigo a jam’iyyar APC Josef Onoh, ya ce shekaru takwas da tsohon shugaba Muhammadu Buhari ya yi a kan karagar mulki na tattare da cin hanci da rashawa da kuma rashin tsaro.
Onoh ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani ga Buhari na cewa Nijeriya ta samu ci gaba sosai a harkokin tsaro da tattalin arziki a lokacin mulkinsa.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa lokacin da ya karbi mulki tattalin arzikin Nijeriya ya rushe tare da matsalar tsaro a hannun jam’iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki.
Buhari, ya tabbatar da cewa a dabarun gwamnatinsa sun yi nasarar magance wadannan matsaloli, tare da dakile ayyukan ta’addanci da matsalolin tattalin arziki.