![]() |
Ahmad Aliyu |
Gwamnatin jihar Sokoto ta ware sama da Naira miliyan 998 domin shirin ciyarwar watan azumin Ramadan na shekarar 2025.
Gwamnan jihar Ahmed Aliyu, a yayin kaddamar da shirin, ya jaddada kudirin gwamnatin na fadada shirin domin isa ga al'umomin jihar baki daya.
Ya ce ko a shekarar da ta gabata irin wannan aiki na ciyarwa a cibiyoyi sama da 130 a fadin jihar.
A cewar sa a wannan shekarar a kara adadin zuwa cibiyoyi 155 don rage cunkoson wuraren da ake da su tare da tabbatar da saukin samun abinci ga masu azumi.