![]() |
Abba Kabir Yusuf |
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature D/Tofa, ya fitar ranar Talata.
Gwamnan ya yi alkawarin ne a lokacin lokacin da ya karbi rahoto daga shugaban kwamitin da aka kafa da daya gudanar da bincike kan zanga zangar da aka gudanar a ranar 1 ga Agusta, 2024, bisa jagorancin mai shari’a Lawan Wada (mai ritaya), yayin taron majalisar zartarwa ta jihar Kano daya gudana a gidan gwamnati ranar Talata.
Rahoton kwamitin ya ce akalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu bakwai suka samu munanan raunuka a jihar Kano.
A cewar rahoton an kuma lalata kadarorin gwamnati da daidaikun mutane da suka haura N11bn a lokacin zanga zangar.