Gwamnatin jihar Bauchi ta ba da hutun makarantu saboda gabatowar watan Ramadan

 

Bala Muhammad Abdukadir

Gwamnatin jihar Bauchi, ta hannun ma’aikatar ilimi ta sanar da rufe dukkanin makarantun jihar a shirye shiryen fara azumin watan Ramadan na 2025 na tsawon makonni biyar.

Hakan na kunshe a cikin wata sanarwar da ma'aikatar ilimi ta jihar ta fitar.

Da yake zantawa da Kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN), jami’in yada labarai na ma’aikatar ilimin Jalaludeen Maina ya ce dama tun kafin wannan lokaci aka sanya yadda tsarin hutun zai kasance a cikin kalanda.

Ya bayyana cewa fara hutun zai fara ne daga ranar 1 ga Maris har zuwa 5 ga Afrilu wanda ya kama sati biyar kenan.

Maina ya ce hutun ya shafi dukkanin makarantun da suka hada da na gwamnati da masu zaman kansu na firamare da na sakandare da kuma manyan makarantun jihar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp