![]() |
Malam Umar Namadi |
Kwamishinan yada labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu Sagir Ahmed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an amince da hakan ne a yayin zaman majalisar zartaswar jihar.
Ahmed ya ce an yanke hukuncin ne bisa shawarwarin da kwamitin kula da makarantu, cibiyoyin lafiya, da kotuna suka bayar.
Ya ce majalisar zartawar ta amince da rahoton kwamitin da ya ba da shawarar daukar matakan kariya don tabbatar da tsaro ga dukkanin makarantun firamare da sakandare, manyan kotuna, cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko, da manyan asibitoci a fadin jihar.