Da yake zantawa da Hajj Reporters, shugaban riko na hukumar alhazzai musulmai ta jihar Abdulrazaq Diepriye ya ce, gwamnan ya biya kudin mutanen tare da tallafin da zai taimaka musu wajen yin aikin hajjin 2025.
Diepriye ya kuma bayyana cewa Gwamna Fubara ya biya wa kudin ne kafin wa’adin da hukumar NAHCON ta sanya ya cika.
A cewarsa, ko a shekarar da ta gabata gwamnan ya biya wa wasu mutanen kujerun aikin hajji domin su sauke farali.
Category
Labarai
Allah yayi mashi sakayya da alherinsa
ReplyDelete