![]() |
Gwamnatin jihar Katsina ta kashe naira biliyan 5.4 don tallafa wa mata 3,610 su yi kiwon awaki a fadin jihar, kowacce ta samu akuya hudu.
Gwamna Dikko Radda ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da rabon tallafin a karkashin shirin kiwon akuya a Dan Nakolo da ke karamar hukumar Daura.
Gwamnan ya bayyana cewa wannan bikin wani gagarumin ci gaba ne a harkar noma a jihar, kuma wani mataki ne na tabbatar da aniyar ganin jihar Katsina ta zama jagora a fannin dogaro da kai a fadin yankin Arewa da Nijeriya baki daya.
A cewarsa, shirin bayar da akuyoyin wani muhimmin bangare ne na dabarun bunkasa kiwon dabbobi, da inganta samar da abinci da samar da dama mai dorewa ga manoma.