![]() |
Abba Kabir Yusuf |
Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi gargadi ga malaman makarantu da kada su umurci dalibai yin ayyuka masu tsauri a ciki ko wajen makaranta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ga manema labarai.
Gwamnan ya jaddada cewa makarantu wajen ba da ilimi ne da jagoranci, kyautata ɗabi’a ba wajen bautar da dalibai ba.
A wata ziyarar bazata da gwamnan ya kai wata makarantar koyar da larabci da ke Kano, ya tarar da dalibai su na aiki mai wahala a cikin makarantar .
A bayyane gwamnan ya nuna rashin jin daɗi, tare da tambayar shugaban makarantar game da sanya dalibai irin waɗannan ayyuka.