![]() |
Abba Kabir Yusuf |
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano ya kaddamar da kwamitin da zai bincike matsalolin rashin biyan albashi da ya shafi wasu ma'aikatan gwamnati a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Alhamis ya bayyana matakin a matsayin cin zarafin ma’aikata da ba za a amince da shi ba da kuma cin amanar al'umma,gwamnan ya sha alwashin fallasa tare da hukunta wadanda suke da hannu wajen aikata hakan.
Ya ce gwamnati ba za ta amince da duk wani zalunci da ake yi wa ma’aikatan ta ba, duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan rashin imani tabbas, zai fuskanci fushin doka.
An umurci kwamitin da ya gudanar da cikakken bincike kan albashin jihar daga Oktoba 2024 zuwa Fabrairu 2025, gano ma’aikatan da abin ya shafa, tantance su, tare da ba da shawarar gyara.