Gwamnan jihar Plateau Mutfwang ya dakatar da hakar ma'adinai a jihar

Gwamnan jihar Plateau a Najeriya Caleb Mutfwang ya sanya wa wata doka hannu da ta haramta hakar ma'adinai a fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a wannan Assabar 22 ga Fabrairu a fadar gwamnatin jihar.

Mutfwang yace daukar matakin dakatar da hakar ma'adinan na da nasaba da kokarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar tare da kare muhalli da kuma kubutar da yara daga aikin karfi.

Haka zalika gwamnan ya kafa kwamitin da zai yi duba akan hakar ma'adinan ta re da bada shawarwarin sauya akalar hakar ma'adinan a jihar, karkashin jagorancin kwamishinan shari'a na jihar Barista Philemon Dafi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp