Gwamnan jihar Kano Engr. Abba Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta jihar

 

Abba Kabir Yusuf/Aminu Abdussalam

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu a kan dokar ne a yayin zaman majalisar zartaswa ta jihar da ya gudana a ranar Talata 18/2/2025.

Hakan na zuwa ne makwanni biyu bayan majalisar dokokin jihar Kano ta zartar da kuduri bayan yin mahawara mai zurfi akan kudurin.

A cikin wasu tanade tanaden dokar, ta baiwa rundunar tsaron damar yakar miyagun laifuka, za kuma su gudanar da ayyukansu a fadin jihar.

Sanya hannu kan dokar shi ne mataki na karshe na tabbatar da ita a hukumance yayin da ake sa ran hukumomi za su sanar da tsarin daukar ma'aikatan rundunar, da kuma nadin wadan da za su jagoranci rundunar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp