![]() |
Bola Ahmad Tinubu |
Fadar shugaban Najeriya ta ware Naira Biliyan daya da Miliyan 99, domin samar da wutar lantarki a fadar cikin shekarar 2025.
Hakan ya biyo bayan tsaiko da aka samu na saka wuta mai amfani da hasken Rana ta Solar da aka shirya fara amfani da ita tun a watan Disambar 2024 da Janairu 2025, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.
Rahoton ya ce a cikin watannin farkon shekarar 2024, fadar ta kashe sama da Miliyan 88 don siyen man na Diesel.
A binciken da Jaridar ta ce ta yi ta gano yadda aka biya kamfanin Fetur na Emmahaly Naira Miliyan 40, domin samar da litar man na Diesel lita 30,000 da aka yi Amfani dashi a Asibitin fadar sai dakin saukar Baki na ofishin mataimakin shugaban kasa.
Haka zalika an biya kamfanin AYM Shafa Naira Miliyan 12, Kudin samar da Man na Lita 10, ga Asibitin cikin fadar kamar yadda bayanai suka tabbatar a cewar Jaridar.
A Ranar 20 ga Mayun 2024, an sake biyan Kamfanin na AYM Shafa kan man da ya samar har karo biyu a Ranar 14 ga Maris na 2024.Biyan na farko shi ne Naira Miliyan 26 na Kudin litar mai 20,000 , sai sai Miliyan 8 na cikon kudin Lita 20,000.