![]() |
Alhaji Aliko Dangote |
Yanzu haka dai yawan kudin Dangote wanda shi ne mutumin da ya fi kudi a nahiyar Afrika sun kai Dalar Amurka bilyan 23.9.
Hakan na zuwa ne bayan da matatar man Dangote da aka gina da kudi Dala bilyan 20 ta fara aiki shekarar da ta gabata a birnin Lagos.
A shekarar 2024, Dangote mai shekaru 67 na da kudin da suka kai Dala bilyan 13.4.