Dan wasan Madrid David Alaba ya sake tafiya jinyar rauni

 

David Alaba

Dan wasan Real Madrid David Alaba ya sake samun rauni a kafarsa ta dama, kwanaki kadan bayan dawowar sa daga jinya.

Fabrizio Romano ya rawaito cewa Real Madrid ta tabbatar da samun raunin dan wasan na ta a kafarsa ta dama, kuma zai yi jinyar kusan makonni biyu zuwa uku.

Tun bayan tafiyar dan wasan jinya a wacan lokaci Madrid ta sha fama da matsalar wanda zai maye gurbin dan wasan,zuwa yanzu Raul Asencio da Vallejo sune ake ganin kungiyar za ta iya ci gaba da amfani da su kafin dawowar dan wasan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp