Dan majalisar wakilai daga jihar Kebbi ya bar PDP ya koma jam'iyyar APC

 


Dan Majalisar wakilai mai wakiltar Besse/Maiyama daga jihar Kebbi, Salisu Garba Koko, ya bar PDP zuwa jam’iyyar APC.

Salisu Koko ya bayyana sauya shekar tasa ne a wata wasika da ya aike wa majalisar kuma kakakin majalisar, Abbas Tajudeen ya karanta.

Dan majalisar a wasikar ta sa, ya bayyana cewa ficewar ta sa baya rasa nasaba da rikicin cikin gida da ya dade yana addabar jam'iyyar PDP.

Ficewar Koko na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da wani dan jam’iyyar daga jihar Kaduna, Amos Magaji, ya fice daga babbar jam’iyyar adawa, bisa dalilin makamancin haka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp