Hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce dakarun sojin kasar sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kuma kame masu laifi 198 tare da kubutar da mutane 93 da aka yi garkuwa da su a cikin makon da ya gabata.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, Daraktan yada labarai na rundunar, Maj-Gen Markus Kangye, ya ce sojojin sun kuma kwato manyan makamai 86 da kuma kananan makamai 2,040 a hannun 'yan ta'adda a fadin kasar.
Category
Labarai