Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sha alwashin cewa nan ba da dadewa ba za a kawar da fitaccen shugaban ‘yan fashin dajin nan da ya addabi yankin arewacin Nijeriya, Bello Turji.
Olufemi Oluyede ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, yayin da yake ganawa da manema labarai a hedikwatar Operation Hadarin Daji.
Ya ce ‘yan ta’addan da ake nema ruwa a jallo irin su Bello Turji suna ci gaba da buya, duba da irin wutar da suke sha, kuma duk inda suka je sai an kawar da su.
Category
Labarai