![]() |
Dr. Adekunle Raif |
Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan Dr. Adekunle Raif Adeniji, inda suka dage cewa sai an biya su adadin kudin da suke nema kafin sakin sa.
Daily Trust ta zanta da makusancin sa inda ya ce har yanzu daraktan da sauran mutanen suna hannun masu garkuwar kuma wadanda suka yi garkuwa da su sun ce ba za a sake shi ba har sai an biya kudin.
Makonni biyu da suka gabata ne dai wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogi kirar AK-47 suka yi garkuwa da Dr Adeniji a unguwar Chikakore da ke Kubwa, a cikin karamar hukumar Bwari da ke Abuja.