'Yan ta'adda da ba a tantance yawansu ba, sun kai hari a kauyen Mai Bakko na karamar hukumar Sabuwa a jihar Katsina.
Lamarin kamar yadda majiyar DCL Hausa ta shaida, ya faru ne a daren Laraba, lokacin da barayin dajin suka afka wa garin da harbin kan mai uwa da wabi.
Bayanai sun ce mutane 5 sun rasa rayukansu ta dalilin wannan harin, yayin da aka yi awon gaba da mutane 7.
Majiyar ta ce maza da mata ne barayin dajin suka yi nasarar arcewa da su bayan farmakin da suka kai.
Garin Mai Bakko dai, na da nisan kilomita 7 zuwa hedikwatar karamar hukumar Sabuwa ta jihar Katsina.
Duk a cikin daren na Laraba ne dai wasu barayin kuma suka afka garin Tsiga ba karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, inda suka yi awon-gaba da tsohon Darakta Janar na hukumar NYSC Janar Maharazu Tsiga da karin wasu mutane 10.
Har ya zuwa lokacin hada wannan labari, hukumomi ba su uffan ba game da lamurran. Amma dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina DSP Sadiq Aliyu Abubakar ya shaida wa DCL Hausa cewa zai bincika.