Barayin daji sun sace liman da "mamu" a lokacin sallar asuba a jihar Sokoto


Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da sace musulmai masu yawa a lokacin da suke sallar asuba a kauyen Bushe na karamar hukumar Sabon Birni ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa'i ya tabbatar wa da jaridar Punch.

Bayanai dai sun ce barayin dajin sun farmaki masallatan ne a lokacin da suke sallar asuba, suka saci mutane 10 ciki hada limamin da ke jan sallar.

Lamarin dai ya faru ne da asubar Alhamis din makon nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp